عن النعمان بن بشير رضي الله عنه مرفوعاً: «لَتُسَوُّنَّ صُفُوفَكُم أو لَيُخَالِفَنَّ الله بين وُجُوهِكُم». وفي رواية: «كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يُسَوِّي صُفُوفَنَا، حتى كَأَنَّمَا يُسَوِّي بها القِدَاح، حتَّى إِذَا رأى أَنْ قد عَقَلْنَا عَنهُ، ثم خَرَج يومًا فَقَام، حتَّى إِذَا كاد أن يُكَبِّرُ، فَرَأَى رَجُلاً بَادِيًا صَدرُهُ، فقال: عِبَادَ الله، لَتُسَوُّنَّ صُفُوفَكُم أو لَيُخَالِفَنَّ الله بين وُجُوهِكُم».
[صحيح] - [الرواية الأولى: متفق عليها. والرواية الثانية: رواها مسلم]
المزيــد ...

Daga Nu'aman Dan Bashir zuwa ga Annabi: "Wallahi ko dai ku daidaita Sahunku ko kuma Allah ya saba tsakanin Fuskokinku" a wata Riwayar kuma: "Manzon Allah ya kasance yana daidaita sawunmu, har kace yana jera tukwane ne, har sai idan cewa yaga lallai mun fahimce shi, sannan ya fito wata rana sai ya tsaya, sai da ya kusa yayi kabbara, sai yaga wani Mutum ya turo kirjinsa waje, sai, Sai ya ce: kodai ku daidaita sahunku ko kuma Allah ya saba tsakanin fuskokinku"
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya tabbatar da cewa idan dai ba'a daidaita sahun Sallah ba to zai sassaba fuskokin wadan da sahun su ya karkace basu kuma daidaita shi ba, cewa lallai lokacin da wasu zasu wuce gaban wasu a sahu, kuma su bar kofofi a tsakaninsu, kuma Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana koyar da sahabbansa da magana kuma ya shiryar da su da aiki, don ya tsaya yana daidaita su da Hannunsa, hai sai da Annabi ya tabbatar sun fahimci shi kuma sun koya, a cikin wata Sallah daga cikin Salloli sai yaga wani daga cikin Sahabbansa ya turo cikinsa a sahu a tsakanin Abokan Sallar sa sai Annabi yayi fushi kuma ya ce : " kodai ku daidaita Sahunku ko kuma Allah ya sassaba tsakanin fuskokinku".

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin