عن عبد الله بن بُحَيْنَةَ رضي الله عنه وكان من أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم «أن النبي صلى الله عليه وسلم صلَّى بهم الظهر فقام في الركعتين الأُولَيَيْنِ، ولم يَجْلِسْ، فقام الناس معه، حتى إذا قضى الصلاة وانتظر الناس تسليمه: كَبَّرَ وهو جالس فسجد سجدتين قبل أن يُسَلِّمَ ثُمَّ سَلَّمَ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Buhaina-Allah ya yarda da shi- ya kasance cikin sahabban Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- "Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-yayi musu sallar Azahar sai ya mike daga raka'a biyun farko, bai yi zaman tahiya ba, si mutane suka mike tare da shi,har aka kammala salla, mutane suka jira sallamarsa: sai yayi kabbara yana daga zaune sai yayi sujjada guda biyu kafin yayi sallama,sannan sai yayi sallama".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayiwa Sahabbansa Sallar Azahar,yayinda ya sallaci raka'oi biyun farko,sai ya tashi a bayansu,bai yi zaman Tahiya na farko ba,sai Mamu suka bishi a bisa hakan.Har sai da ya sallaci raka'o'i biyun karshe,kuma ya zauna don Tahiyar karshe,ya gama ta,Mutane suka jirayi sallamarsa,sai yai kabbara alhali yana cikin zamansa,sai yayi sajada dasu sajadu biyu kafin yayi sallama kwatankwacin sajadar cikin Salla,sannan yayi sallama.wannan sajadar ta kasance gyara ga Tahiyar da ya bari.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin