+ -

عن أبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قال: «صلَّى بنا رسول الله صلى الله عليه وسلم إحدى صَلاتَيْ الْعَشِيِّ -قال ابن سِيرِينَ وسمَّاها أبو هُرَيْرَةَ، ولكن نسيت أنا- قال: فصلَّى بنا ركعتين، ثم سلَّم، فقام إلى خَشَبَةٍ مَعْرُوضَةٍ في المسجد، فَاتَّكَأَ عليها كأنه غضبان ووضع يده اليُمنى على اليُسرى، و شَبَّكَ بين أصابعه، وخرجت السَّرَعَانُ من أبواب المسجد فقالوا: قَصُرَتِ الصلاة -وفي القوم أبو بكر وعمر- فهابا أن يكلماه، وفي القوم رجل في يديه طُول، يقال له: ذو اليدين فقال: يا رسول الله، أنسيت؟ أم قَصُرَتِ الصلاة؟ قال: لم أَنْسَ وَلَمْ تُقْصَرْ، فقال: أكما يقول ذو اليدين؟ فقالوا: نعم، فتقدَّم فصلَّى ما ترك، ثم سلَّمَ، ثم كبَّر وسجد مثل سجوده أو أطول، ثم رفع رأسه فكبَّر، ثم كبَّر وسجد مثل سجوده أو أطول، ثم رفع رأسه وكبَّر، فربما سألوه: ثم سلّم؟ قال: فَنُبِّئْتُ أن عِمْرَانَ بْنَ حُصَيْنٍ قال: ثم سلَّمَ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abihurairata Allah ya kara yarda a gareshi ya ce: { Manzon Allah mai tsira da aminchi yayi mana daya daga cikin sallolin isha guda biyu- ibnu sirin ya ce haka Abu hurairata ya ambace su.saidai ni na manta- ya ce sai yayi mana sallah raka`ah biyu, sa`annan yayi sallama .sai ya tashi izuwa wata itaciya da ta fito a cikin masallachin, sai ya kishingida akan wannan itaciya kamar yana cikin fushi sai ya dora hannun sa na dama akan na hagu, sai ya saqa tsakanin yan yatsun sa.sai suka ce: an rage raka`o`in salla ne? a cikin mutanen akwai Abubakar da Umar sai suks ji nauyin yimasa magana. kuma a cikin su akwai wani mutum mai tsawon hannu, ana kiransa zulyadaini sai ya ce: ya manzon Allah, kayi mantuwa ne? ko kuma sallar ta ragu ne? sai ya ce: ban manta ba kuma ba`a rage ba. sai ya ce da su: shin abinda zulyadaini ya fada haka ne? sai suka ce eh, haka ne: sai ya shiga gaba ya sallaci abinda ya bari sai yayi sallama, sa`annan yayi kabbara yayi sujjada kwatankwacin sujjadar sa ko sama da haka . sa`annan ya daga kansa yayi kabbara sannan ya kuma yin kabbara yayi sujjada kwatankwacin sujjadarsa ko sama da haka sa`annan ya dago kansa yayi kabbara sau da yawa suna tambayar sa:sa
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Maazanni sune mafi cikar hankalin Mutane, kuma sune mafi tabbatar zukata, kuma sune mafi tsayuwa da hakkin Allah, amma duk da hakan basu futa daga iyakar Mutane ba, Mazon allah shi ne mafi cikar sifofi, kuma duk da haka wani lokaci Mantuwa takan bujuro masa, sabida kasancewa dan adam ne, kuma Abu huraira ya rawaito cewa Annabi yayi sallah da sahabbansa kodai Sallar azahar ko kuma La'asar kuma cewa Abu Huraira ya fade ta amma kuma Dan Sereen ya manta ta, yayin da yayi Sallah Raka'a biyu na farko sai ya yi Sallama, kuma yayin da ya kasance Annabi Mutum ne cikakke, ransa ba zai nutsu ba sai da cikakken aiki, sai yaji a jikinsa cewa akwai tawaya da kuma wani abu bai cika ba, kuma baisan mai ya jawo shi ba, sai ya tashi zuwa wani ita cce da aka ajiye a gaban alkiblar Masallacin kuma ya kashingida a kansa ransa yana sosuwa, kuma ya hade yan yatsunsa, kuma masu saurin futa daga Masallaci suka futa suna ganawa a tsakaninsu, cewa wani abu ya faru fa, shi ne an rage Sallah, kamar sunji nauyin Annabi ne cewa yaya zai yi kamarsa yayi mantuwa, kuma sabida kwarjininsa a zukatansu babu wanda ya iya bugar kirji da ya tambaye shi akan wannan Mai muhimmanci, cikin wadanda suke wurin har da Abubakar da Umar -Allah ya yarda da su, Musamman daman sun lura da damuwarsa da kuma kebancewarsa, sai dai wani Mutum daga cikin Sahabbai ana kiran Zulyadainshi ya yanke wannan shiru din, ta hanayar tambayarsa Annabi da cewa: Ya Manzon Allah wai Mantawa kayi ne? domin babu wanda ya iya tambaya kowanne ya yanke cewa wannan hakan zai iya faruwa, sai Annabi ya ce: yana mai gini zatonsa, ba'a rage ba kuma ba mantawa nayi ba, sai Annabi yai nufin ya tabbatar da ingancin abinda zulyadaini yake fada, domin ya sabawa zaton sa na cewa Sallar ta cika ko bata cika ba ne abinda zai rinjayar da fadinsa, sai ya ce ga wadanda suke gefensa na Sahabbansa: Haka yake abinda Zulyadain yake fada raka'a biyu kawai nayi? sai suka ce: Ey a lokacin sannan Annabi ya shige gaba ya kawo abinda ya bari na ragowar sallar, kuma bayan yayi tahiya sai yayi sallama sannan yayi Kabbara kuma yana zaune, kuma yayi Sujada kwatankwacin sujadar ainahin Sallah ko mafi tsawo daga ita, sannan ya dago kansa sannan yayi kabbara, sannan ya kuma yin kabbara kuma yayi sujada kwatankwacin sujada ko mafi tsawonta, sannan ya kuma dago kansa kuma yayi kabbara, sannan yayi sallama kuma bai tahiya ba.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Portuguese
Manufofin Fassarorin