+ -

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِذَا شَكَّ أَحَدُكُمْ فِي صَلَاتِهِ، فَلَمْ يَدْرِ كَمْ صَلَّى ثَلَاثًا أَمْ أَرْبَعًا، فَلْيَطْرَحِ الشَّكَّ، وَلْيَبْنِ عَلَى مَا اسْتَيْقَنَ، ثُمَّ يَسْجُدُ سَجْدَتَيْنِ قَبْلَ أَنْ يُسَلِّمَ، فَإِنْ كَانَ صَلَّى خَمْسًا شَفَعْنَ لَهُ صَلَاتَهُ، وَإِنْ كَانَ صَلَّى إِتْمَامًا لِأَرْبَعٍ كَانَتَا تَرْغِيمًا لِلشَّيْطَانِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 571]
المزيــد ...

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Idan ɗayanku ya yi kokwanto a cikin sallarsa, bai san nawa ya sallata ba shin uku ne ko huɗu, to ya watsar da kokwanton, ya yi gini akan abinda ya yi yaƙini, sannan ya yi sujjada, sujjada biyu kafin ya yi sallama, idan ya kasance ya sallaci raka'a biyar za su yi masa shafa'in sallarsa, idan ya kasance ya yi sallar dan cika huɗun to sun zama turbuɗe hancin Shaiɗan".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 571]

Bayani

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mai sallah idan ya yi taraddudi a cikin sallarsa bai san nawa ya sallata ba, shin uku ne ko huɗu? to ya nisantar da adadin da ya yi kokwanto cikinsa kada ya yi anfani da shi; ukun su ne abin da aka yi yaƙini akan su, sai ya sallaci raka'a ta huɗu, sannan sai ya yi sujjada kafin ya yi sallama.
Idan abinda ya sallata huɗu ne a haƙiƙa; to sun zama biyar in an kara raka'ar, sajadodi biyun na rafkanuwa canji ne ga raka'a, sai adadin ya zama biyu kenan ba ɗaya ba, idan kuma ya sallaci huɗu ne da wannan raka'ar ta ƙari; sai ya zama ya bada abinda ke kansa ba tare da ƙari ko ragi ba.
Sujjada biyun na rafkanuwa sun zama ƙasƙantarwa ga Shaiɗan da kuma halakarwa gare shi, da dawo da shi a taɓe abin nisantarwa daga manufarsa; domin shi ya cakuɗa masa sallarsa, ya bijiro dan ɓata ta, kuma sallar ɗan Adam ta cika yayin da ya yi riko da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki - da yin sujjadar da Iblis ya saɓa maSa da ita, lokacin da ya ki biyayya ga Allah da yin sujjada ga (Annabi) Adam.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Mai sallah idan ya yi kokwanto a cikin sallarsa, sai kuma bai iya rinjayar da ɗayan abu biyun gare shi ba, to anan ya watsar da kokwanton ya yi aiki da yaƙini, shi ne mafi ƙaranci, sai ya cika msallarsa ya yi sujjada kafin ya yi sallama, sannan ya yi sallama.
  2. Waɗannan sujjadun biyu hanya ce zuwa gyara sallah, da mayar da Shaiɗan a taɓe ƙasƙantacce abin nisantarwa daga manufarsa.
  3. Kokwanton da yake cikin Hadisin shi ne kaikawo ba tare da rinjayarwa ba, idan an sami zato kuma ya yi rinjaya sai a yi aiki da shi.
  4. Kwaɗaitarwa akan yaƙar waswasi da tunkuɗe shi ta hanyar ruko da umarnin shari'a.