عن عائشةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رضي الله عنها:
أن النبي صلى الله عليه وسلم كان لا يَدع أربعا قَبل الظهر وركعتين قبل الغَدَاة.
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 1182]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -:
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba).
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1182]
Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana lazimta akan sallolin nafilfili a ɗakinta kuma ba ya barinsu: Raka'o'i huɗu da sallama biyu kafin sallar Azahar, da kuma raka'o'i biyu kafin sallar Asuba.