lis din Hadisai

"Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa"
عربي Turanci urdu
Na kiyaye raka'o'i goma daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -*: Raka'a biyu kafin Azahar, da raka'a biyu a bayan azahar, da raka'a biyu bayan Magariba a gidansa, da raka'a biyu bayan Issha' a gidansa, da raka'a biyu kafin sallar Asuba, wani lokaci ne ba'a shiga wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa, Nana Hafsat ta zantar da ni cewa idan ladani ya yi kiran sallah, alfijir ya bullo zai yi sallah raka'a biyu, a wani lafazin: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana sallah bayan Juma'a raka'a biyu.
عربي Turanci urdu
Mun kasance muna shirya wa Manzon Allah - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - kayan aikin sa da tsarkake shi, saboda haka Allah zai aiko masa da duk abin da yake son ya aiko daga dare, don haka sai ya sa su daidai, ya yi alwala ya yi sallah.
عربي Turanci urdu
Cewa Annabi –SAW- ya kasance yana bacci a farkon dare, yana tashi a qarshen dare yana sallah
عربي Turanci urdu
Idan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya rasa salla daga jin zafi ko wani abu da daddare, zai yi raka’a goma sha biyu da rana.
عربي Turanci urdu
A kowane dare Annabi yana wutiri ko a farkon dare ko tsakiyarsa, ko karshensa, Kuma yakan tsaida Wutirinsa da Asuba
عربي Turanci urdu
"Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci".
عربي Turanci urdu
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba).
عربي Turanci urdu
"Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi ".
عربي Turanci urdu
"Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna".
عربي Turanci urdu
Na ganka kana sallah banda sumba? Ya ce: Da ban ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - na aikata abin da na aikata ba
عربي Turanci urdu
Cewa Lallai Annabi ya Kasance yana Tasbihi akan abin hawansa, kuma ko ina ya sanya fuskarsa, yana nuni da kansa, kuma haka ma Dan Umar yake yi
عربي Turanci urdu
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr.
عربي Turanci urdu
Idan Dayankuya tashi cikin dare, sai ya Harshensa ya fara Nauyi wajen karanta Kur'ani, bai san mai yake Karantawa ba to ya Kwanta
عربي Turanci urdu
Mutumin kirki Abdullah, da idan da dare yayi yana tashi yayi sallah
عربي Turanci urdu
Annabi ya kasance -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- da Abubakar da Umar sunayin Sallar Idi kafin Huduba
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya yi barci a madadin jam’iyyarsa da daddare, ko wani kan abu daga ciki, to karanta shi tsakanin sallar asuba da sallar azahar
عربي Turanci urdu
"Idan dayanku yayi gyagyadi a cikin Sallah to ya kwanta har sai baccin ya tafi"
عربي Turanci urdu
"Dayanku yayi Sallah cikin Nishadi, Idan kuma ya gaji to yayi kwanciyarsa"
عربي Turanci urdu
"Mun Kasance idan Muka sauka Masauki, Bama tasbihi har sai mun sauke kaya"
عربي Turanci urdu
Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi- ya umarce mu da mu fito sallar idi guda biyu yara mata da suka fara wayo da `yan matan da ake tsarewa cikin dakuna a cikin gidaje, ya kuma umarci mata masu haila da su nisaci wuraren sallah na musulmi
عربي Turanci urdu
Ya Ubangiji na miqa Wuyana zuwa gareka, kuma nayi Imani da kai, kuma na dogara a gareka, kuma na kawo qara zuwa gareka, kuma gareka nake neman Hukunci, to kayi mun gafarar abunda na gabatar da wanda na jinkirta, da kuma abunda na Voye da wanda na bayyana, da abunda kafi ni sani da shi a tare da ni, Babu Ubangiji sai kai
عربي Turanci urdu
An rawaito daga Anas -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Mun Kasance idan Muka sauka Masauki, Bama yin Sallah har sai mun sauke kaya"
عربي Turanci urdu
Naga Manzon Allah SAW yana Sallah a cikin qirjinsa da wani Ruri Kamar Rurin Dutsen Niqa saboda Kuka SAW
عربي Turanci urdu
Manzon Allah ya yi tsayuwar dare da Aya xaya daga cikin Qur'ani
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
na kwana a wajan Gwaggwona Maimuna,sai Manzan Allah ya tashi yana salla da daddare,sai na tsaya a hagunsa,sai ya ruko kaina ya tsayar dani a damansa
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koya mana Istikhara a cikin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Alƙur'ani*, yana cewa: «Idan ɗayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi (sallah) raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce: Ya Allah ni ina neman zaɓinKa da saninKa, kuma ina neman ikonKa da ikonKa, ina roƙonKa daga falalarKa mai girma, domin cewa Kai Kana da iko ni ba ni da iko, kuma Kana sani ni kuma bani da sani, kaine Masanin abinda ke ɓoye, ya Allah idan Kasan cewa wannan al'amarin alheri ne a cikin Addinina, da rayuwata da ƙarshen al'amarina» ko cewa ya yi: "Magaggaucin al'amarina da kuma majirkincinsa, to ka kaddara mini shi kuma ka sawwaka mini shi sannan Ka yi albarka gareni a cikinsa, idan kuma Kasan cewa wannan al'amarin sharri ne gareni a cikin Addinina da rayuwata da karshemn al'amarina" ko cewa ya yi: "A cikin magaggaucin al'amarina da majirkincinsa, to ka kawar da shi daga gareni ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alheri a duk inda yake, sannan Ka yarda da ni" Ya ce: "Sai ya ambaci buƙatarsa».
عربي Turanci urdu