عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مُغَفَّلٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم:
«بَيْنَ كُلِّ أَذَانَيْنِ صَلَاةٌ، بَيْنَ كُلِّ أَذَانَيْنِ صَلَاةٌ» ثُمَّ قَالَ فِي الثَّالِثَةِ: «لِمَنْ شَاءَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 627]
المزيــد ...
Daga Abdullahi dan Mugaffal - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"A kwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu, akwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu" sannan ana uku ya ce: "Ga wanda ya so".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 627]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa akwai sallar nafila tsakanin kowanne kiran sallah da iƙama, kuma ya maimaita hakan sau uku, kuma ya bada bayani ana ukun cewa hakan mustahabbi ne ga wanda ya yi nufin yin sallah.