عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنهما أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ قَالَ حِينَ يَسْمَعُ النِّدَاءَ: اللَّهُمَّ رَبَّ هَذِهِ الدَّعْوَةِ التَّامَّةِ، وَالصَّلاَةِ القَائِمَةِ، آتِ مُحَمَّدًا الوَسِيلَةَ وَالفَضِيلَةَ، وَابْعَثْهُ مَقَامًا مَحْمُودًا الَّذِي وَعَدْتَهُ، حَلَّتْ لَهُ شَفَاعَتِي يَوْمَ القِيَامَةِ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 614]
المزيــد ...
Daga Jbir ɗan Abbdullahi - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Duk wanda ya ce a yayin da ya ji kiran sallah: (Ya Allah, Ma’abocin wannan cikakken kira da sallah da za'a tayar, Ka bai wa [Annabi] Muhammad al-Wasila da al-Fadila, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo wanda Ka yi masa alƙawarin sa), ceto na zai halatta a gare shi ranar alƙiyama".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 614]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah bayan ya gama:
(Ya Allah Ma’abocin wannan kiran) sune lafuzan kiran sallah waɗanda ake kira zuwa bautar Allah da kuma sallah da su, (cikakkiya) cikakkiya, kira zuwa ga Tauhidi da saƙo, (da sallar da za'a tayar) dawwamammiya wacce za'a tayar, (Ka bawa) Ka bawa, ((Annabi) Muhammad al-Wasila) matsayi maɗaukaki a cikin aljanna wanda ba ya kamata sai gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, (da Fadila) daraja ce mai ƙaruwa akan darajoji kan halittu, (Ka tashe shi) Ka ba shi (matsayi abin yabo) wanda ake yabon mai tsayawa a cikinsa; shi ne babban ceto a ranar alƙiyama, (wanda Ka yi masa alƙawari) da faɗinKa: {Ana kaunar Ubangijinka ya tasheka a wani matsayi abin yabo} da ya kasance gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Wanda ya yi wannan addu'ar ya cancanci kuma ceton Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajaba a gare shi ranar alƙiyama.