عن أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيَّ رَضِيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهُ صلَّى اللهُ عليهِ وَسَلَّم:
«لَقِّنُوا مَوْتَاكُمْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 916]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ku laƙƙanawa matattunku: Laa ilaha illallah»
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 916]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitarwa kan mu faɗi kuma mu maimaita kalamr Tauhidi "La'ilaha illallahu" a wurin wanda fizgar mutuwa ta zo masa har sai ya faɗeta, dan ta zama ƙarshen maganarsa.