1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهُما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«البَسُوا مِنْ ثِيَابِكُمُ البَيَاضَ، فَإِنَّهَا مِنْ خَيْرِ ثِيَابِكُمْ، وَكَفِّنُوا فِيهَا مَوْتَاكُمْ».

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu".

Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shi Sunan Tirmizi - 994

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana shiryar da maza cewa su sa tafafi masu farin launi da kuma yi wa mamata likkafani a cikinsu; domin cewa sune mafi alherin tufafi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so sanya farin tufafi, kuma waninsa na wata kalar ma yana halatta.
  2. An so yi wa mamata likkafani da fararen (tufafi).
  3. Shaukani ya ce: Hadisin yana nuni akan halaccin sanya fari da yi wa mamata likkafani da shi; kasancewarsa ya fi waninsa tsarkaka, amma kasancewarsa ya fi tsarki to wannan zahiri ne, amma kasancewarsa ya fi tsafta domin cewa mafi ƙanƙatar abu idan ya faɗa kansa zai bayyana sai ya fifita.

Manufofin Fassarorin

35 Yare
EN English الإنجليزية
ID Indonesia الإندونيسية
BN বাংলা البنغالية
TR Türkçe التركية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
FA فارسی الفارسية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
MY မြန်မာ البورمية
TH ไทย التايلندية
PS پښتو بشتو
AS অসমীয়া الأسامية
SQ Shqip الألبانية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية