عَنْ مَطَرِ بْنِ عُكَامِسٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِذَا قَضَى اللَّهُ لِعَبْدٍ أَنْ يَمُوتَ بِأَرْضٍ جَعَلَ لَهُ إِلَيْهَا حَاجَةً».

[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 2146]
المزيــد ...

Daga Madar Dan Ukamis - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Idan Allah Ya kaddarawa bawa cewa zai mutu a wata kasa sai Ya sanya masa wata bukata zuwa gareta".

[Ingantacce ne] - [Tirmizi ne ya ruwaito shi] - [Sunan Tirmizi - 2146]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah idan Ya hukunta Ya kuma kaddarawa bawa cewa zai mutu a wata kasa alhali shi ba ya cikin kasar; sai a sanya masa wata bukata gareta sai ya tafi kasar, sai a karbi ransa a cikinta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hadisin gasgatawa ne ga fadin Allah - Mai girma da daukaka -: {Kuma wata rai ba ta sanin a wacce kasa zata mutu}.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (65)