+ -

عَنْ طَاوُسٍ أَنَّهُ قَالَ: أَدْرَكْتُ نَاسًا مِنْ أَصْحَابِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُونَ كُلُّ شَيْءٍ بِقَدَرٍ، قَالَ: وَسَمِعْتُ عَبْدَ اللهِ بْنَ عُمَرَ رضي الله عنهما يَقُولُ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«كُلُّ شَيْءٍ بِقَدَرٍ، حَتَّى الْعَجْزِ وَالْكَيْسِ، أَوِ الْكَيْسِ وَالْعَجْزِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2655]
المزيــد ...

Daga Dawus cewa shi ya ce: Na riski wasu mutane daga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna cewa kowane abu (yana kasancewa) da kaddara ne, ya ce: Na ji Abdullahi Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su, yana cewa: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
"Kowanne abu da kaddara ne, har gajiya da dabara, ko kuma wayo da gajiya ".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2655]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa kowanne abu da kaddara ne; Har kasawa: ita ce: Barin abinda yake wajibi ne aikata shi, da cewa zai yi ta jinkirta shi daga lokacinsa, da al'amuran duniya da lahira. Har dabara ita ce: Nishadi da kwarewa da al'amuran duniya da lahira. Kuma cewa Allah - Mai girma da daukaka - hakika Ya kaddara gajiyawa da wayo da kowane abu, ba zai afku a kasantacce ba sai hakika sanin Allah Ya rigaya da shi da mashi'arSa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy الفولانية Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin kudircewar sahabbai - Allah Ya yarda da su - a kaddara.
  2. Kowanne abu yana faruwa ne da kaddarawar Allah har gajiyawa da kuma nishadi.
  3. Ya tabbata kuma sahabbai - Allah Ya yarda da su, sun tsoratar - a cikin riwayar hadisan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  4. Yin imani da kaddara dukkaninsa alherinSa da kuma sharrinSa.