عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ رضي الله عنهما قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«كَتَبَ اللهُ مَقَادِيرَ الْخَلَائِقِ قَبْلَ أَنْ يَخْلُقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِخَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ، قَالَ: وَعَرْشُهُ عَلَى الْمَاءِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2653]
المزيــد ...
Daga Abdullahi dan Amr dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Allah Ya rubuta abinda ya kaddarawa halittu kafin Ya halicci sammai da kasa da shekara dubu hamsin, ya ce: Al’ArshinSa yana kan ruwa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2653]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa , Allah Ya rubuta abinda zai afku na abinda ya kaddarawa halittu a fayyace, na rayuwa da mutuwa da arziki da makamancin hakan a cikin Lauhul mahfuz , tun kafin ya halicci sammai da kasa da shekara dubu hamsin, abin yana afkuwane daidai da dacewar abinda Allah - mai girma da daukaka - Ya hukunta, Dukkanin wani abu mai kasancewa to da hukuncin Allah ne da ikonSa, Abinda ya samu bawa bai zama zai kuskure shi ba, abinda ya kuskure shi bai zama zai same shi ba.