+ -

عن ابن عباس رضي الله عنهما قال:
كُنْتُ خَلْفَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَوْمًا، فَقَالَ: «يَا غُلَامُ، إِنِّي أُعَلِّمُكَ كَلِمَاتٍ، احْفَظِ اللهَ يَحْفَظْكَ، احْفَظِ اللهَ تَجِدْهُ تُجَاهَكَ، إِذَا سَأَلْتَ فَاسْأَلِ اللهَ، وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاللهِ، وَاعْلَمْ أَنَّ الْأُمَّةَ لَوِ اجْتَمَعَتْ عَلَى أَنْ يَنْفَعُوكَ بِشَيْءٍ، لَمْ يَنْفَعُوكَ إِلَّا بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللهُ لَكَ، وَلَوِ اجْتَمَعُوا عَلَى أَنْ يَضُرُّوكَ بِشَيْءٍ، لَمْ يَضُرُّوكَ إِلَّا بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللهُ عَلَيْكَ، رُفِعَتِ الْأَقْلَامُ وَجَفَّتِ الصُّحُفُ».

[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 2516]
المزيــد ...

Daga ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana, sai ya ce: "Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka sameshi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah, ka sani cewa da al'umma za su taru a kan su amfaneka da wani abu, ba za su amfaneka ba sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta maka, da za su taru a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su cutar da kai ba, sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta a kanka, an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe".

Ingantacce ne - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi

Bayani

Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana ba da labarin cewa ya kasance yana ƙarami yana haye tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce: Zan sanar da kai wasu al'amura da wasu abubuwan da Allah zai amfanar da kai su:
Ka kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninsa da nisantar hane-hanensa, ta inda Zai sameka a ayyukan biyayya da kusanci, ka da Ya sameka a ayyukan saɓo da zunubai, idan ka aikata haka sakamakonka zai kasance shi ne Allah Zai kiyayeka daga abubuwan ƙi na duniya da lahira, kuma Zai taimakeka a ayyukanka a duk inda ka fuskanta.
Idan kayi nufin roƙon wani abu, to, kada ka roƙi kowa sai Allah, to, haƙiƙa Shi kaɗai ne wanda yake amsawa masu roƙo.
Idan kayi nufin neman taimako, to, kada ka nemi taimakon kowa sai Allah.
Kuma ya zama kana da yaƙini cewa wani amfani ba zai sameka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya sun taru akan amfanarka sai dai abin da Allah Ya rubuta maka, kuma wani abin cutarwa ba zai faru a kanka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya za su taru a kan cutarka, sai dai abin da Allah Ya ƙaddara a kanka.
Kuma wannan al'amarin tabbas Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya rubuta maka ya kuma ƙaddara shi daidai da abin da hikimarsa da saninsa suka hukunta, babu canji ga abin da Allah Ya rubuta.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية القيرقيزية النيبالية اليوروبا الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية الكينياروندا الرومانية المجرية التشيكية المالاجاشية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Muhimmancin sanar da yara al'amuran addini na tauhidi da ladubba da sauransu.
  2. Sakamako yana kasancewa daga irin aikin da aka yi.
  3. Umarni a kan dogaro ga Allah, da tawakkali gareshi ba da waninsa ba, madalla da Shi a matsayin wakili.
  4. Imani da hukunci da ƙaddara da yarda da shi, kuma Allah Ya ƙaddara kowane abu.
  5. Wanda ya tozarta umarnin Allah, to, Allah Zai tozartashi ba zai kiyayeshi ba.