عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«مَنْ كَذَبَ عَلَيَّ مُتَعَمِّدًا فَلْيَتَبَوَّأْ مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 110]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi masaukinsa a wuta".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] - [Sahih Al-Bukhari - 110]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya yi masa karya da gangan ta hanyar danganta masa magana ko aiki, to lallai cewa shi yana da mazauni a wuta; sakamako ne gare shi akan karyar da ya yi masa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Karya ga - Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da nufi da ganganci sababi ne na shiga wuta.
  2. Karya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba kamar karya ce ga sauran mutane ba, saboda abinda ke tattare da hakan na barnace-barnace masu girma a Addini da duniya.
  3. Tsoratarwa akan yada hadisai kafin tabbatar da ingancin dangantasu ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (55)