عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«بَلِّغُوا عَنِّي وَلَوْ آيَةً، وَحَدِّثُوا عَنْ بَنِي إِسْرَائِيلَ وَلَا حَرَجَ، وَمَنْ كَذَبَ عَلَيَّ مُتَعَمِّدًا فَلْيَتَبَوَّأْ مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 3461]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ku isar game da ni koda aya daya ce, kuma ku zantar game da Banu Isra'ial babu laifi, duk wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi mazauninsa a wuta".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3461]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umarni da isar da ilimi daga gare shi na littafi ne ko Sunnah, koda abin ya zama kadan ne kamar aya daya daga Alkur’ani ko hadisi, da sharadin ya zama masani da abinda zai isarda shi kuma ya yi kira zuwa gare shi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa babu laifi da akan bayanai daga Banu Isra'il da abinda ya afku gare su na al'amura da abinda ba ya karo tare da shari'a. Sannan ya yi gargadi daga yi masa karya, kuma cewa duk wanda ya yi masa karya da gangan to yariki masauki a wuta.