عن عبدِ الله بن عمرو رضي الله عنهما قال:
كنتُ أكتبُ كلَّ شيءٍ أسمعُه من رسولِ الله صلَّى الله عليه وسلم أُريدُ حفْظَه، فنهتْني قريشٌ، وقالوا: أتكْتبُ كلَّ شيءٍ تَسمَعُه من رسول الله صلَّى الله عليه وسلم، ورسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم بَشَرٌ يتكلَّمُ في الغضَبِ والرِّضا؟ فأمسَكتُ عن الكتاب، فذكرتُ ذلك لرسول الله صلَّى الله عليه وسلم، فأومأ بإصبَعِه إلى فيه، فقال: «اكتُبْ، فوالذي نفسي بيدِه، ما يَخرُجُ منه إلا حقٌّ».
[صحيح] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 3646]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Na kasance ina rubuta dukkan abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son haddace shi, sai Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Shin ka dinga rubuta dukkan abin da ka ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, alhali Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin fushi da yarda? sai na dakata daga rubutun, sai na fadawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hakan sai ya yi nuni da 'yan yatsunsa zuwa bakinsa, sai ya ce: "Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya".
[Ingantacce ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 3646]
Abdullah ɗan Amr - Allah Ya yarada da su - ya ce: Na kasance ina rubuta dukkanin abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - don na haddace shi a rubuce, sai wasu mutane daga Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin yarda da fushi, zai iya yin kuskure, sai na daina rubutun.
Sai na ba wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - labarin abin da suka faɗa, sai ya yi nuni da danyatsansa zuwa bakinsa, sai ya ce; Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da yake fita daga cikinsa sai gaskiya a kowanne hali, haka a halin yarda da fushi.
Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa game da AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Ba ya magana bisa son rai* shi (Alƙur'ani) ba wani abu ba ne ba ban da wahayi da ake saukar masa) [Al-najm 3-4].