+ -

عَنْ سَمُرَةَ بْنِ جُنْدَبٍ وَالْمُغِيرَةِ بْنِ شُعْبَةَ رضي الله عنهما قَالَا: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ حَدَّثَ عَنِّي بِحَدِيثٍ يُرَى أَنَّهُ كَذِبٌ، فَهُوَ أَحَدُ الْكَاذِبِينَ».

[صحيح] - [رواه مسلم في مقدمته]
المزيــد ...

Daga Samura ɗan Jundub da Mugira ɗan Shu'ubah - Allah Ya yarda da su - sun ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata".

[Ingantacce ne] - - [صحيح مسلم]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya riwaito wani Hadisi daga gare shi alhali shi yana sane ko yana zato ko yana rinjayar da zatansa cewa shi Hadisin ƙaryane a gare shi- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; to maruwaicinsa yana tarayya da mai ƙirƙirar wannan ƙaryar.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الرومانية Malagasy
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Tabbatar da Hadisan da aka ruwaito daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da tabbatar da ingancinsu kafin ruwaitosu.
  2. Siffar ƙarya ana sakinta ne ga dukkan wanda ya ƙirƙiri ƙarya da kuma wanda ya tsaya ya yadata da watsata tsakanin mutane.
  3. Ruwaito Hadisin ƙarya yana haramta akan wanda ya san kasancewarsa ƙarya ne, ko kuma ƙaryarsa ta rinjaya a zatonsa sai dai in ya kasance dan gargadi ne daga gare shi .