عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ:
«إِيَّاكُمْ وَالظَّنَّ؛ فَإِنَّ الظَّنَّ أَكْذَبُ الْحَدِيثِ، وَلَا تَحَسَّسُوا، وَلَا تَجَسَّسُوا، وَلَا تَحَاسَدُوا، وَلَا تَدَابَرُوا، وَلَا تَبَاغَضُوا، وَكُونُوا عِبَادَ اللهِ إِخْوَانًا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6064]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Na haneku da zato; domin cewa zato shi ne mafi karyar zance, kada ku yi binciken (aibobin mutane), kada ku yi hassada, kada kujuyawa juna baya, kada ku yi kiyayya, ku zama bayin Allah 'yan uwa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6064]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani, yana gargadarwa daga sashin abinda yake kaiwa zuwa rabuwa da gaba a tsakanin musulmai, daga cikin hakan:
(Zato) shi ne tuhumane da yake faruwa a cikin zuciya ba tare da wani dalili ba, ya kuma bayyana cewa shi ne mafi karyar zance.
Da (Bincike): Shi ne bincike game al'aurorin mutane ta hanyar gani ne ko kasa kunne.
Da (bincike): Shi ne bincike daga abinda ya boyu daga al'amura, mafi yawan abinda ake fada a (Tajassus) a sharri ne.
Da kuma: Game da (hassada) ita ce kin samuar ni'ima ga wasu.
Da kuma: (Juyawa juna baya) shi ne sashi ya bijirewa sashi, ba zai yi sallama ba, ba zai ziyarci dan'uwansa musulmi ba,
Da kuma: (kiyayya da juna) kiyayya da gujewa, kamar cutar da wasu ne, da daure fuska da mummunar tarba.
Sannan ya fadi wata kalma wacce ta tattaro halayen Musulmai sashinsu tare da sashi da za ta gyara su ita ce:(ku zama bayin Allah 'yan uwa). 'Yan uwantaka tana kulla alakoki dake tsakanin mutane, da suke haduwa da ita, kuma tana kara soyayya da sabawa a tsakaninsu.