Karkasawa: Falaloli da Ladabai .
+ -

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«سِبَابُ المُسْلِمِ فُسُوقٌ، وَقِتَالُهُ كُفْرٌ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 48]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 48]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya zagi ɗan uwansa musulmi, kuma hakan yana daga fasiƙanci shi ne fita daga yi wa Allah ɗa'a da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma yaƙar musulmi ga ɗan uwansa musulmi yana daga ayyukan kafirci, sai dai hakan kafirci ne ƙarami.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الرومانية Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wajabcin girmama mutuncin musulmi da jininsa.
  2. Girman lamarin zagin musulmi ba tare da wani haƙƙi ba; to mai zagin ba tare da wani haƙƙi ba fasiƙi ne.
  3. Zagin musulmi da yaƙarsa yana raunana imani kuma yana tauye shi.
  4. Sashin ayyuka ana ambatansu kafirci; koda basu kai ga kafirci babba mai fitarwa daga tafarkin Musulunci ba.
  5. Abin nufi da kafirci a nan kafirci ƙarami wanda ba ya fitarwa daga Addini da haɗuwar Ahlus Sunnah; domin Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya tabbatar da 'yan uwantaka ta imani ga muminai a halin yaƙi tsakaninsu da kuma jayayyarsu, sai Allah Maɗaukakin sarki Ya ce; {Idan ƙungiyoyi biyu ta muminai suka yi faɗa to ku yi sulhu a tsakaninsu} zuwa faɗinSa; {Kaɗai muminai 'yan uwa ne}.