عن حذيفة رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول:
«لَا يَدْخُلُ الْجَنَّةَ قَتَّاتٌ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6056]
المزيــد ...

Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa;
"Annamimi ba zai shiga aljanna ba".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] - [Sahih Al-Bukhari - 6056]

Bayani

(Annabi) Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana ba da labarin cewa annamimi wanda yake cirato zance a tsakanin mutane da nufin ɓata tsakaninsu shi mai cancanta ne ga uƙubar cewa ba zai shiga aljanna ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Annamimanci yana daga manyan zunubai.
  2. Hani daga annamimanci; saboda abin da ke cikinsa na ɓatawa da cutarwa a tsakaknin ɗaiɗaiku da jama'u.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (67)