kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

Kada ku rubuta komai daga gare ni, kuma duk wanda ya rubuta wani abu daga gare ni ba Qur'ani ba to ya goge shi, kuma ku zantar daga gare ni kada ku samu damuwa, kuma duk wanda yayi mun qarya yana sane to ya tanadi mazauninsa a Wuta
عربي Turanci urdu
"Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su"
عربي Turanci urdu
Na kasance ina rubuta dukkan abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son haddace shi, sai Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Shin ka dinga rubuta dukkan abin da ka ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, alhali Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin fushi da yarda? sai na dakata daga rubutun, sai na fadawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hakan sai ya yi nuni da 'yan yatsunsa zuwa bakinsa, sai ya ce: "@Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya".
عربي Turanci urdu