عن أَنَسَ بْنَ مَالِكٍ رضي الله عنه قال:
بينما نحن جلوس مع النبي صلى الله عليه وسلم في المسجد دخل رجل على جمل، فأناخه في المسجد ثم عقله، ثم قال لهم: أيكم محمد؟ والنبي صلى الله عليه وسلم متكئ بين ظهرانيهم، فقلنا: هذا الرجل الأبيض المتكئ. فقال له الرجل: يا ابن عبد المطلب فقال له النبي صلى الله عليه وسلم: «قد أجبتك». فقال الرجل للنبي صلى الله عليه وسلم: إني سائلك فمشدد عليك في المسألة، فلا تجد علي في نفسك؟ فقال: «سل عما بدا لك» فقال: أسألك بربك ورب من قبلك، آلله أرسلك إلى الناس كلهم؟ فقال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن نصلي الصلوات الخمس في اليوم والليلة؟ قال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن نصوم هذا الشهر من السنة؟ قال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن تأخذ هذه الصدقة من أغنيائنا فتقسمها على فقرائنا؟ فقال النبي صلى الله عليه وسلم: «اللهم نعم». فقال الرجل: آمنت بما جئت به، وأنا رسول من ورائي من قومي، وأنا ضمام بن ثعلبة أخو بني سعد بن بكر.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 63]
المزيــد ...
Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su: Waye Muhammad a cikinku? alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide a tsakaninsu, sai muka ce : Wannan farin mutumin wanda ke kishingide. Sai mutumin ya ce da shi: Ya kai Dan Abdul Mudallib sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: "Hakika na amsa maka". Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji haushi na a ranka? sai ya ce: "Ka tambayi abinda ya bayyana gareka" sai ya ce: Ina tambayarka dan Ubangijinka da Ubangijin wadanda suka gabaceka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane gaba dayansu? sai ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu yi salloli biayr a yini da dare? ya ce: "Eh ya Allah ne.” ya ce Ina maka magiya da Allah shin Allah ne Ya umarceka da mu yi azumin wannan watan a shekara? ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce; Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawan mu? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Eh ya Allah". sai mutumin ya ce; na yi imani da abinda ka zo da shi, kuma ni manzo ne na wadanda ke bayana cikin mutane na, Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 63]
Anas dan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa: Lokacin da sahabbai suna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci yayin da wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya durkusar da rakumin sannan ya daure shi. Sannan ya tambayesu: Waye Muhammd a cikinku? Alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide tsakanin mutanen, sai muka ce : Wannan farin mutumin. Sai mutumin ya ce da shi: Yakai Dan Abdul Muddalib. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: Na ji ka yi tambaya in amsa maka. Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne kuma mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji wani abu game dani a ranka. Wato: Kada ka yi fushi da ni kuma kada kunci ya sameka. Sai ya ce: Ka tambayi abinda kake so. Sai ya ce: Ina ina hada ka da Ubangijinka kuma Ubangijin wadanda suka gabace ka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane? Sai ya ce: Eh ya Allah, dan karfafa gaskiyarsa. Sai Mutumin ya ce: Ina yi maka magiya da Allah, wato; Ina tambayarka sabo da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka yi salloli biyar a yini da dare? Su ne salloli wadanda aka faralanta ?., Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu azimci wannan watan daga shekara? wato: Watan Ramadan, Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka daka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawanmu? ita ce zakka. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Eh ya Allah, Sai Dimam ya musulunta, kuma ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa shi zai kira mutanensa zuwa Musulunci. Sannan ya yi bayanin kansa cewa shi ne Dimam dan Sa'alabata daga Banu Sa'ad Ibnu Bakar.