عَنْ زِيَادِ بْنِ لَبِيدٍ رضي الله عنه قَالَ:
ذَكَرَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ شَيْئًا، فَقَالَ: «ذَاكَ عِنْدَ أَوَانِ ذَهَابِ الْعِلْمِ» قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، وَكَيْفَ يَذْهَبُ الْعِلْمُ، وَنَحْنُ نَقْرَأُ الْقُرْآنَ وَنُقْرِئُهُ أَبْنَاءَنَا وَيُقْرِئُهُ أَبْنَاؤُنَا أَبْنَاءَهُمْ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ؟ قَالَ: «ثَكِلَتْكَ أُمُّكَ زِيَادُ، إِنْ كُنْتُ لَأُرَاكَ مِنْ أَفْقَهِ رَجُلٍ بِالْمَدِينَةِ، أَوَلَيْسَ هَذِهِ الْيَهُودُ وَالنَّصَارَى يَقْرَؤونَ التَّوْرَاةَ وَالْإِنْجِيلَ، لَا يَعْمَلُونَ بِشَيْءٍ مِمَّا فِيهِمَا؟!».
[صحيح لغيره] - [رواه ابن ماجه] - [سنن ابن ماجه: 4048]
المزيــد ...
Daga Ziyad Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wani abu, sai ya ce: "Wannan a lokacin tafiyar ilimi kenan" Na ce: Ya Manzon Allah, ta yaya ilimi zai tafi, alhali mu muna karanta Alkur’ani kuma, muna karantar da 'ya'yanmu shi, kuma 'ya'yanmu suna karantar da 'ya'yansu har zuwa ranar Alkiyama ? Ya ce: "Mahaifiyarka ta yi wabinka Ziyad, na kasance ina ganinka daga mafi fahimtar mutane a Madina, shin wadannan Yahudawan da Nasaran ba sa karanta Attaura da Injila, ba sa aiki da wani abinda ke cikinsu?!".
[Ingantacce ne ta wani bangaren] - [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi] - [سنن ابن ماجه - 4048]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya kasance a zaune tsakanin sahabbansa, sai ya ce:: Wannan lokacin da za'a dauke a zare ilimi ne daga mutane. Sai Ziyad Dan Labid Al-Ansary - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamaki kuma ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya ce; Ta yaya za'a dauke ilimi a sarayar da shi daga garemu?! Alhali mun karanta Alkur’ani mun haddaceshi; na rantse da Allah sai mun karantashi, kuma mun karantar da matanmu da 'ya'yanmu shi, da 'ya'yan 'ya'yanmu, Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce yana mai mamaki: Mahaifiyarka ta rasaka ya Ziyad! na kasance ina lissafaka daga malaman mutanen Madina! Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana masa: Cewa rasa ilimi bai zamo da rasa Alkur’ani ba; saidai rasa ilimi (yana kasancewa ne) da rashin aiki da shi, Wannan Attaurar da Injilar dake wajen Yahudawa da Nasara; a tare da haka ba ta anfanesu ba, kuma ba su anfana da manufarsu ba; shi ne aiki da abinda suka sani.