عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «إِذَا سَمِعتُم المُؤَذِّن فَقُولُوا مِثلَ مَا يَقُول».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Amru Dan Ass - Allah ya yarda da su-zuwa ga Annabi -In kuka ji mai kiran salla na yin kiran salla to ku fadi irin abin da yake fada
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Idan kuka ji mai kiran sallah to ku amsa masa, ku rika maimaita irin abin da ya fada, daidai da daidai, in yayi kabbar a to kuma ku yi bayan ya yi, in yayi sahada biyu to kuma ku yi, za ku sami irin ladan da ya tsere muku na rashin yin kiran sallar da ladani ya yi, Allah mai yalwar kyauta ne kuma masu amsa addu'a