عَنْ المُغِيرَةِ رضي الله عنه قَالَ:
كُنْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَأَهْوَيْتُ لِأَنْزِعَ خُفَّيْهِ، فَقَالَ: «دَعْهُمَا، فَإِنِّي أَدْخَلْتُهُمَا طَاهِرَتَيْنِ» فَمَسَحَ عَلَيْهِمَا.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 206]
المزيــد ...
Daga Mugira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wata tafiya, sai na sunkuyo don in cire masa huffi, sai ya ce: "Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki" sai ya yi shafa akansu.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 206]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a daya daga tafiye-tafiyensa sai ya yi alwala, lokacin da ya isa wanke kafafuwa sai Mugira dan Shu'uba - Allah Ya yarda dashi - ya mika hannayensa dan ya cire abinda ke saman kafar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - na kuffi dan wanke kafafuwansa, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka barsu kada ka cire su, ni na shigar da kafafuwamna a cikin kuffin alhali ni ina da tsarki (Alwala). Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shafa akan kuffinsa, maimakon wanke kafafuwa kenan.