عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَنَمَةَ، قَالَ:
رَأَيْتُ عَمَّارَ بْنَ يَاسِرٍ دَخَلَ المَسْجِدَ فَصَلَّى، فَأَخَفَّ الصَّلَاةَ، قَالَ: فَلَمَّا خَرَجَ، قُمْتُ إِلَيْهِ، فَقُلْتُ: يَا أَبَا اليَقْظَانِ، لَقَدْ خَفَّفْتَ، قَالَ: فَهَلْ رَأَيْتَنِي انْتَقَصْتُ مِنْ حُدُودِهَا شَيْئًا؟! قُلْتُ: لَا، قَالَ: فَإِنِّي بَادَرْتُ بِهَا سَهْوَةَ الشَّيْطَانِ، سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَقُولُ: « إِنَّ الْعَبْدَ لَيُصَلِّي الصَّلَاةَ، مَا يُكْتَبُ لَهُ مِنْهَا إِلَّا عُشْرُهَا، تُسْعُهَا، ثُمُنُهَا، سُبُعُهَا، سُدُسُهَا، خُمُسُهَا، رُبُعُهَا، ثُلُثُهَا نِصْفُهَا».
[حسن] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 18894]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Ibnu Anamah, ya ce:
Na ga Ammaru Ibnu Yasir ya shiga masallaci sai ya yi sallah, sai ya sauƙaƙa sallar (wato bai dadeba), ya ce: Lokacin da ya fita, sai na tashi zuwa gare shi, sai na ce: Ya Aba Yaƙazan, haƙiƙa ka sauƙaƙa, ya ce: Shin ka ga na rage wani abu daga ka’idojinta?! Na ce: A'a, ya ce: Lallai ni na gaggautata ne dan gudun waswasin shaiɗan, na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «Lallai bawa zai yi sallah, ba za'a rubuta masa wani abu daga gareta ba sai ushurinta (daya cikin goma), sai ɗaya bisa taranta, sai ɗaya bisa bakwanta, sai ɗaya bisa shidanta, sai ɗaya bisa biyar ɗinta, sai ɗaya bisa huɗunta, sai ɗaya bisa ukunta, sai rabinta».
[Hasan ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 18894]
Ammar Ibnu Yasir - Allah Ya yarda da su - ya shiga masallaci sai ya yi sallar nafila, kuma sallar ta kasance sassauƙa ce, lokacin da ya fita daga cikin masallaci, sai Abdullahi Ibnu Anamah ya bi shi ya kuma ce da shi: Ya Aba Yaƙazan, haƙiƙa na ganka ka sauƙaƙa sallarka! Ammar ya ce: Shin ka ganni ne na tauye wani abu daga rukunanta ko wajibanta ko sharuɗɗanta?! ya ce: A'a, ya ce: Lallai cewa ni na sauƙaƙata ne tun kafin shaiɗan ya shagaltar da ni. Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai bawa zai yi sallah, amma ba za'a rubuta masa (komai) daga ladanta ba sai ɗaya bisa gomanta, ko ɗaya bisa taranta, ko ɗaya bisa takwas ɗinta, ko ɗaya bisa bakwanta, ko ɗaya bisa shidanta, ko ɗaya bisa biyar ɗinta, ko ɗaya bisa huɗunta, ko ɗaya bisa ukunta, ko rabinta.