kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koya mana Istikhara a cikin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Alƙur'ani*, yana cewa: «Idan ɗayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi (sallah) raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce: Ya Allah ni ina neman zaɓinKa da saninKa, kuma ina neman ikonKa da ikonKa, ina roƙonKa daga falalarKa mai girma, domin cewa Kai Kana da iko ni ba ni da iko, kuma Kana sani ni kuma bani da sani, kaine Masanin abinda ke ɓoye, ya Allah idan Kasan cewa wannan al'amarin alheri ne a cikin Addinina, da rayuwata da ƙarshen al'amarina» ko cewa ya yi: "Magaggaucin al'amarina da kuma majirkincinsa, to ka kaddara mini shi kuma ka sawwaka mini shi sannan Ka yi albarka gareni a cikinsa, idan kuma Kasan cewa wannan al'amarin sharri ne gareni a cikin Addinina da rayuwata da karshemn al'amarina" ko cewa ya yi: "A cikin magaggaucin al'amarina da majirkincinsa, to ka kawar da shi daga gareni ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alheri a duk inda yake, sannan Ka yarda da ni" Ya ce: "Sai ya ambaci buƙatarsa».
عربي Turanci urdu