عن أم عَطيَّة نُسَيْبة الأنصارية رضي الله عنها قالت: «أَمَرَنا رسول الله صلى الله عليه وسلم أن نُخْرِج في العيدين الْعَوَاتِقَ وَذَوَاتِ الْخُدُورِ، وأَمَر الحُيَّض أن يَعْتَزِلْنَ مُصلّى المسلمين».
وفي لفظ: «كنا نُؤمر أن نَخْرُجَ يوم العيد، حتى نُخْرِجَ الْبِكْرَ من خِدْرِهَا، حَتَّى تخرجَ الْحُيَّضُ، فَيُكَبِّرْنَ بتكبيرهم ويدعون بدعائهم، يرجون بَرَكَة ذلك اليوم وطُهْرَتَهُ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
An karbo daga Ummu atiyyah ita ce Nusaibah mutuniyar madina Allah ya kara yadda a gareta ta ce:{manzon Allah tsira da aminci su kara tabbata a gareshi- ya umarcemu da mu fito sallae idi guda biyu yara mata da suka fara wayo da `yan matan da ake tsarewa cikin dakuna a cikin gidaje, ya kuma umarci mata masu haila da su nisaci wuraren sallah na musulmi}. a wani lafazin kuma: {Mun kasance ana umartar mu da mu fito ranar idi, harma mufito da `yan mata daga cikin dakunan su, har da masu haila ma su fito, sai suyi kabbara tare da kabbarar masu sallah suyi addu`ah da addu`ar su, suna masu fatan samun albarkar wannan yini da tsarkins}.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Ranar idin karamar sallah da ranar idin babbar sallah na daga cikin ranaku masu falala, wadanda alamomin musulunci ke bayyana a cikinsu`yan`uwantakar musulmi tana bayyana a fili ta hanyar haduwar su waje daya da tattaruwar su a sahu-sahu, dukkan mutanen gari suna tattaruwa a waje guda don bayyanar da hadin kan su, da haduwar zukatan su, da haduwar kalmar su bisa taimakon addinin musulunci, da daukaka kalmar Allah tare da tsaida ambaton Allah da bayyanar da alamominsa. saboda haka ne annabi mai tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi yayi umarni da a fitowar dukkan mata, harma da dukkan `yan matan da aka suturce su cikin gidajen su fitowar tana kansu, da mata masu jinin haila, saidai zasu zauna ne a nesa da masu sallah, domin su halarci alheri da addu`ar musulmai sai su samu alheran wannan taro, su kuma samu albarka sa, da samun rahamar Allah da yardar sa don rahamar ta kasance da samun karbuwa ta zamo mafi kusa garesu. sallar idi guda biyu farilla ce ta kifaya.