عَنْ بُسْرِ بْنِ سَعِيدٍ، أَنَّ زَيْدَ بْنَ خَالِدٍ الْجُهَنِيَّ رَضيَ اللهُ عنه، أَرْسَلَهُ إِلَى أَبِي جُهَيْمٍ رَضيَ اللهُ عنه، يَسْأَلُهُ مَاذَا سَمِعَ مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي الْمَارِّ بَيْنَ يَدَيِ الْمُصَلِّي؟ قَالَ أَبُو جُهَيْمٍ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَوْ يَعْلَمُ الْمَارُّ بَيْنَ يَدَيِ الْمُصَلِّي مَاذَا عَلَيْهِ لَكَانَ أَنْ يَقِفَ أَرْبَعِينَ خَيْرًا لَهُ مِنْ أَنْ يَمُرَّ بَيْنَ يَدَيْهِ» قَالَ أَبُو النَّضْرِ: لَا أَدْرِي قَالَ: أَرْبَعِينَ يَوْمًا أَوْ شَهْرًا أَوْ سَنَةً؟
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 507]
المزيــد ...
Daga Busr Ibnu Sa'id cewa Zaid Ibnu Khalid al-Juhani - Allah Ya yarda da shi -, ya aike shi zuwa wajen Abu Juhaim - Allah Ya yarda da shi -, yana tambayarsa me ya ji daga wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a sha'anin wanda ya wuce ta gaban mai yin sallah? Abu Juhaim ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Mai wuce wa ta gaban mai sallah da ya san abin da ke kan shi na zunubi, to ya tsaya arba'in shi ne mafi alheri gareshi da ya wuce ta gabansa» Abu-al-Nadhr ya ce: Ban sani ba shin ya ce: Kwanaki arba'in ya ce ko wata ko shekara?
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 507]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga wucewa ta gaban wanda yake sallar farilla ko nafila, kuma cewa da wanda yake aikata haka da gangan da ya san abinda zai haɗu da shi na laifi; da a ce ya zaɓi ya tsaya arba'in; to shi ne mafi alheri gare shi da ya wuce ta gabansa. Abu al-Nadhr maruwaicin hadisin ya ce: Ban sani ba ya ce kwanaki arba'in ne ko wata ko shekara.