عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: كان قِرَام لعائشة سَترت به جانب بَيتها، فقال النبي صلى الله عليه وسلم : «أَمِيطِي عنَّا قِرَامَكِ هذا، فإنه لا تَزال تصاوِيُره تَعْرِض في صلاتي».
[صحيح] - [رواه البخاري]
المزيــد ...
Daga Anas bin Malik - Allah ya yarda da shi - ya ce: Labule ne da A’isha ta ke rufe gefen gidanta, Sai Manzon Allah SAW ya ce: "Ki xaukemun wannan labulen naka, saboda hotunan sa suke har yanzu a cikinSallah ta"
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi]
A'isha - Allah ya yarda da ita - tana da siririn mayafin ulu mai launuka da rubutu, wanda da ita ta rufe wani rami da ke cikin dakinta, don haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umurce ta da ta cire shi ya bayyana mata dalilin hakan kuma cewa rubutunta da launuka suna nan suna bayyana a gaban idanunsa a cikin salla, don haka yana tsoron kada hakan ya dauke masa hankali daga kamala. Kasantuwar zuciya a cikin salla, da gudanar da ambatonta, tilawa da niyyar sallamawa ga Allah Madaukaki.