عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهما:
سَأَلَ رَجُلٌ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ عَلَى المِنْبَرِ، مَا تَرَى فِي صَلاَةِ اللَّيْلِ، قَالَ: «مَثْنَى مَثْنَى، فَإِذَا خَشِيَ الصُّبْحَ صَلَّى وَاحِدَةً، فَأَوْتَرَتْ لَهُ مَا صَلَّى» وَإِنَّهُ كَانَ يَقُولُ: «اجْعَلُوا آخِرَ صَلاَتِكُمْ وِتْرًا» فَإِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَمَرَ بِهِ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 472]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -:
Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alokacin yana kan mimbari, me kake gani a kan sallar dare, sai ya ce: «Biyu-biyu ce», idan ya ji tsoron (ɓullowar) Asuba sai ya sallaci raka'a ɗaya, sai ta yi masa wutirin abin da ya sallata» kuma shi ya kasance yana cewa «Ku sanya ƙarshen sallarku ta zama witiri» domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da shi.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 472]
Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tattaba agare shi - a lokacin yana huɗuba akan mimbari: Ya Manzon Allah ka sanar da ni yaya zan yi sallar dare? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka yi sallah ka sallame daga kowadanne raka’oi biyu, idan ka ji tsoron ɓullowar asuba to ka sallaci raka'a ɗaya sai ta yi maka wutirin abin da ka sallata, kuma cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wasicci da a sanya ƙarshen sallar dare ta zama witiri.