عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه:
أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَرَأَ فِي رَكْعَتَيِ الْفَجْرِ: {قُلْ يَا أَيُّهَا الْكَافِرُونَ}، وَ{قُلْ هُوَ اللهُ أَحَدٌ}.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 726]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta
{قل يأيها الكافرون} da {قل هو الله أحد}
a raka'o'i biyu (kafin sallar) Asuba.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 726]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son a raka'o'i biyu na nafilar Asuba, a raka'a ta farko ya karanta surar {قل يأيها الكافرون} [al-Kafirun]. A raka'a ta biyu kuma surar {قل هو الله أحد} [al-Ikhlas].