عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ لِبِلاَلٍ عِنْدَ صَلاَةِ الفَجْرِ:
«يَا بِلاَلُ، حَدِّثْنِي بِأَرْجَى عَمَلٍ عَمِلْتَهُ فِي الإِسْلاَمِ، فَإِنِّي سَمِعْتُ دَفَّ نَعْلَيْكَ بَيْنَ يَدَيَّ فِي الجَنَّةِ» قَالَ: مَا عَمِلْتُ عَمَلًا أَرْجَى عِنْدِي أَنِّي لَمْ أَتَطَهَّرْ طَهُورًا، فِي سَاعَةِ لَيْلٍ أَوْ نَهَارٍ، إِلَّا صَلَّيْتُ بِذَلِكَ الطُّهُورِ مَا كُتِبَ لِي أَنْ أُصَلِّيَ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1149]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce wa Bilal yayin sallar Asuba:
"Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka aikata shi a cikin musulunci, domin ni na ji takun takalmanka a gabana a cikin aljanna" Ya ce: Ban taɓa aikata wani aiki ba mafi kwaɗayi a gurina sai dai cewa bana yin wata alwala a lokacin dare ko rana, sai na sallaci abin da aka rubuta mini in sallata da wannan alwalar.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1149]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin mafarki ya gan shi a cikin aljanna, sai ya cewa Bilal Ibnu Rabah: Bani labarin mafi kwaɗayin aikin nafilar da ka aikata shi a cikin Musulunci? Domin ni na ji ƙarar takalmanka a hankali lokacin da kake motsasu kana tafiya a gabana a cikin aljanna. Bilal ya ce: Ban aikata wani aiki ba mafi kwaɗayi a wurina sai dai cewa ni ban taɓa yin kari (hadasi) ba da daddare ko da rana ba face sa na yi alwala, sannan na yi sallah saboda Ubangijina, ta nafilfili kai tsaye abin da aka rubuta mini in sallata da wannan alwalar