عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: إِذَا حَدَّثْتُكُمْ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَلَأَنْ أَخِرَّ مِنَ السَّمَاءِ أَحَبُّ إِلَيَّ مِنْ أَنْ أَكْذِبَ عَلَيْهِ، وَإِذَا حَدَّثْتُكُمْ فِيمَا بَيْنِي وَبَيْنَكُمْ فَإِنَّ الحَرْبَ خَدْعَةٌ، سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«يَأْتِي فِي آخِرِ الزَّمَانِ قَوْمٌ حُدَثَاءُ الأَسْنَانِ سُفَهَاءُ الأَحْلاَمِ، يَقُولُونَ مِنْ خَيْرِ قَوْلِ البَرِيَّةِ، يَمْرُقُونَ مِنَ الإِسْلاَمِ كَمَا يَمْرُقُ السَّهْمُ مِنَ الرَّمِيَّةِ، لاَ يُجَاوِزُ إِيمَانُهُمْ حَنَاجِرَهُمْ، فَأَيْنَمَا لَقِيتُمُوهُمْ فَاقْتُلُوهُمْ، فَإِنَّ قَتْلَهُمْ أَجْرٌ لِمَنْ قَتَلَهُمْ يَوْمَ القِيَامَةِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3611]
المزيــد ...
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi -: Idan na zantar da ku wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ace in faɗo daga sama shi ya fi soyuwa gareni daga in yi masa (Annabi) ƙarya, idan na zantar da ku a abinda yake tsakanina da ku to lallai yaƙi ɗan yaudara ne, na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
«Wasu mutane zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru masu raunin hankula, suna faɗin mafi alherin zancen halitta (suna yawaita karatun Alƙur'ani), zasu fita daga Musulunci kamar yadda kibiya take fita daga abin da aka harba, imaninsu ba zai ƙetare maƙogwaransu ba, a duk inda kuka gamu da su to ku kashesu, domin kashesu lada ne ga wanda ya kashesu a ranar alƙiyama».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3611]
Sarkin musulmai Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa idan kuka ji ni ina zantar da wani hadisi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lallai cewa ni banayin alkunya bana yin jirwaye mai kama da wanka kuma bana yin tauriyya, kawai ina magana ne ɓaro-ɓaro, kuma a ce in faɗo daga sama shi ya fi sauƙi a gurina daga in zantar da ku wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali ina yi masa ƙarya, idan na yi magana a abinda ke tsakanina da mutane to lallai cewa yaƙi ɗan yaudara ne, saboda haka zan iyayin alkunya ko in yi jirwaye mai kama da wanka ko in yi tauriyya, haƙiƙa na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Wasu matasa zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru, masu raunin hankula, suna faɗin (magana daga) Alƙur'ani kuma suna yawaita karanta shi, zasu fita daga Musulunci kuma su ƙetare iyakokinsa kamar yadda kibiya take fita daga abinda aka harba, imaninsu ba ya wuce maƙogwaransu, a duk inda kuka haɗu da su to ku kashesu, domin cewa kashesu lada ne ga wanda ya kashesu a ranar alƙiyama.