عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَيْسَ الْمُؤْمِنُ بِالطَّعَّانِ وَلاَ اللَّعَّانِ وَلاَ الفَاحِشِ وَلاَ البَذِيءِ».
[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 1977]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Mumini ba mai yawan suka bane ko mai yawan tsinuwa ba ko mai yawan alfasha ba ko mai zancen banza ba".
[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [سنن الترمذي - 1977]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa bai zamo daga sha'anin mumimi mai cikakken imani ya zama mai yawan aibata mutane a cikin dangantakar su ba, kuma ba mai yawan zagi da tsinuwa bane, kuma ba mai yawan alfasha ne da aiki ko magana wacce babu kunya a cikinta ba.