عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«أَتَدْرُونَ مَا الْغِيبَةُ؟»، قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «ذِكْرُكَ أَخَاكَ بِمَا يَكْرَهُ»، قِيلَ: أَفَرَأَيْتَ إِنْ كَانَ فِي أَخِي مَا أَقُولُ؟ قَالَ: «إِنْ كَانَ فِيهِ مَا تَقُولُ فَقَدِ اغْتَبْتَهُ، وَإِنْ لَمْ يَكُنْ فِيهِ فَقَدْ بَهَتَّهُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2589]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce:
"Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka ambaci ɗan uwanka da abin da yake ƙi", aka ce: Shin kana ganin in ya kasance akwai abin da nake faɗa a kan ɗan uwana fa? sai ya ce: "Idan ya kasance a cikinsa akwai abin da kake faɗa, to, haƙiƙa ka yi gibarsa, idan babu (abin da kake faɗa) a cikinsa, to, haƙiƙa ka ƙirƙirar masa ƙarya".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2589]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana haƙiƙanin gibar da aka haramta, ita ce: Ambaton musulmi mai gibar da abin da yake ki, daidai ne ya kasance daga siffofinsa ne na halitta ko na ɗabi'a, kamar: Mai ido ɗaya mai yawan algus maƙaryaci, da makamancin hakan daga siffofin zargi, ko da waɗannan siffofin sun kasance samammu ne a gareshi.
Amma idan babu siffar a tare da shi, to, wannan ya fi tsanani daga giba, shi ne ƙirƙirar ƙarya, wato: Ƙirkirar abin da babu a tare da shi.