عَنِ المُغِيرَةِ بْنِ شُعْبَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لاَ يَزَالُ طَائِفَةٌ مِنْ أُمَّتِي ظَاهِرِينَ، حَتَّى يَأْتِيَهُمْ أَمْرُ اللَّهِ وَهُمْ ظَاهِرُونَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 7311]
المزيــد ...
Daga Mugira Ɗan Shu'uba - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Wasu jama'a daga al'ummata ba za su gushe ba suna masu rinjaye, har sai al'marin Allah ya zo musu alhali su suna masu rinjaye».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 7311]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu mutane ba za su taɓa gushewa ba daga al'ummata suna masu rinjaye akan mutane, masu rinjayar waɗanda suka saɓa musu, hakan har sai al'amarin Allah ya zo musu ta hanyar karɓar rayukansu a ƙarshen zamanin duniya kafin tashin alƙiyama.