عَنْ عَمْرِو بْنِ الحَارِثِ خَتَنِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَخِي أُمِّ المؤمِنين جُوَيْرِيَةَ بِنْتِ الحَارِثِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُم، قَالَ:
مَا تَرَكَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عِنْدَ مَوْتِهِ دِرْهَمًا وَلاَ دِينَارًا وَلاَ عَبْدًا وَلاَ أَمَةً وَلاَ شَيْئًا، إِلَّا بَغْلَتَهُ البَيْضَاءَ، وَسِلاَحَهُ، وَأَرْضًا جَعَلَهَا صَدَقَةً.
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 2739]
المزيــد ...
Daga Amr Ibul Haris ɗan uwan mai dakin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ɗan uwar ummul muminina Juwairiyya Bintul Haris - Allah Ya yarda da su -, ya ce:
Lokacin rasuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai bar dirhami ko dinari ko bawa ko baiwa ko wani abu ba sai farar alfadararsa da makaminsa, da wani filin da ya maida shi sadaka.
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2739]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rasu bai bar dirhamin na azirfaba ko zinari ba, ko bawan da ya mallaka ko baiwar da ya mallaka ko raƙumi ko wani abu na dukiyaba, sai kawai farar alfadararsa wacce yake hawanta, da wani filin da ya bar shi waƙafi a lokacin da yake da lafiya saboda matafiya.