+ -

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ:
كَانَ فِرَاشُ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ أَدَمٍ، وَحَشْوُهُ مِنْ لِيفٍ، وَلِمُسلمٍ: كَانَ وِسَادَةُ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الَّتِي يَتَّكِئُ عَلَيْهَا مِنْ أَدَمٍ حَشْوُهَا لِيفٌ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6456]
المزيــد ...

Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Shimfiɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance ta jemammiyar fata ce, cikinta kaba ne, a Riwayar Muslim kuma : Matashin kai na Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wanda yake dogara a kan shi ya kasance na jemammiyar fata ne, cikinta kaba ce.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6456]

Bayani

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa shimfiɗar da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake kwanciya a kanta ta kasance an yi ta ne da jemammiyar fata, kuma a cike ta ke da kaba ta dabino, haka ma matashinsa wanda yake kishingiɗa a kansa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake a kansa na zuhudu da bijirewa jin daɗin duniya, tare da cewa Allah - tsarki ya tabbatara maSa Ya ɗaukaka - Ya tabbatar masa da hakan inda a ce ya so ya ji daɗin da ita.
  2. Halaccin mallakar shimfiɗa da matashi, da kuma bacci a kansu dan jin sauƙaƙa yin bacci.
  3. Yana kamata ga musulmi ya lura da halinsa da kuma rayuwarsa da halin Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, domin cewa shine abin koyi mai kyau, kuma wanda ya bi tafarkinsa ya shiriya kuma ya rabauta a duniya da lahira.
  4. Kwaɗayi akan yin tanadi domin lahira, kuma mumini ya wadatu da abin da zai taimake shi akan biyayya ga Allah a duniya, kuma kada ya shagalta da neman tara dukiya a duniya, haƙiƙa Allah Ya zargi wasu mutane sai ya ce: {Alfahari (da yawan 'ya'ya da dukiya) ya shagaltar da ku. Har (kuka mutu) kuka ziyarci ƙaburbura} [al-Takasur: 1-2].
Fassara: Turanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Vietnam Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand Asami الهولندية الغوجاراتية الدرية المجرية الجورجية المقدونية الخميرية
Manufofin Fassarorin