عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ:
مَا شَبِعَ آلُ مُحَمَّدٍ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مُنْذُ قَدِمَ المَدِينَةَ مِنْ طَعَامِ البُرِّ ثَلاَثَ لَيَالٍ تِبَاعًا، حَتَّى قُبِضَ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5416]
المزيــد ...

Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basu taɓa ƙoshi daga abincin alkama a darare uku ajere ba tunda ya zo Madina, har aka karɓi ransa.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] - [Sahih Al-Bukhari - 5416]

Bayani

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa iyalan gidan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tun lokacin da Annabi ya zo Madina basu taɓa ƙoshi da alkama ba tsawon kwana uku ajere har (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya koma ga Allah.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Kari (23)