+ -

عن عبد الله بن سلام رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «يَا أَيُّهَا النَّاسُ، أَفْشُوا السَّلَامَ وَصِلُوا الْأَرْحَامَ، وَأَطْعِمُوا الطَّعَامَ، وَصَلُّوا بِاللَّيْلِ وَالنَّاسُ نِيَامٌ، تَدْخُلُوا الْجَنَّةَ بِسَلَامٍ».
[صحيح] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد والدارمي]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An rawaito daga Abdullahi Bn Salam -Allah ya yarda da shi ya ce Naji Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: " Ya Ku Mutane ku yada Sallama, kuma ku sadar da Zumunci, kuma ku ciyar da Abinci, kuma kuyi Sallah Mutane suna bacci, zaku shiga Al-jannah cikin Aminci
Ingantacce ne - Ibnu Majah ne ya Rawaito shi

Bayani

Cikin wannan Hadisi akwai kwadaitarwa da fadakarwa kan Abubuwa Hudu kyawawa da kuma Siffofi Masu kyau ga duk wanda ya sifantu da su to zai shiga Al-janna cikin Amunci, kuma wadan Siffofi sune: Yada Sallama, Sadar da Zumunci, Ciyar da Abinci, Salla cikin dare mutane suna ta shekar bacci, Yada sallama yana nufin: ku bayyana kuma ku yawaita yin Sallamar, kuma ku ciyar da Abinci ga Mabukata, Kamar Iyalanka Matanka da yayanka Maza da Mata da duk wanda yake Gidanka, Kuma idan Mutum ya tashe da Daddare yana Tahajjudi Saboda girman Allah, yana dada kusantar Allah da Maganganunsa da Addu'o'insa yana mai kaskantar da kansa a gabansa, kuma Mutane a halin suna ta Sharar Bacci, to wannan yana daga cikin mafifitan Ayyukan da zasu kaishi Al-janna cikin Amunci, ba tare da Ukuba ba ko Azaba.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin