عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «يقول الله تعالى: أَنَا مَعَ عَبْدِي مَا ذَكَرَنِي وَتَحَرَّكَتْ بِي شَفَتَاهُ».
[صحيح لغيره] - [رواه ابن ماجه وأحمد، ورواه البخاري تعليقاً]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An karbo daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Allah Madaukakin Sarki yana cewa: Ni ina tare da Bawa na ko yaushe ya anbace ni kuma Labbansa suka Motsa saboda ni"
Ingantacce ne ta wani bangaren - Ibnu Majah ne ya Rawaito shi

Bayani

Hadisin yana nuna cewa duk wanda ya tuna Allah to Allah zai kasance kusa da shi, kuma zai kasance tare da shi a kowane Al-amuransa, Saboda zai datar da shi kuma ya shirye shi kuma ya taimake shi ya amsa Addu'arsa, kuma Ma'anar wannan Hadisin ta zo a cikin wani hadisin a cikin sahihul Bukhari Manzon Allah ya ce: "Ni ina inda Bawa na ya Zace ni kuma ni ina tare da shi a duk lokacin da ya anbaceni a , idan ya anbaceni cikin Ransa to zan anbace shi cikin raina, in kuma ya anbace ni cikin Mutane zan anbace shi cikin Mutanen da suka fi nasa Al-kairi

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin