عَن أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَا بَالُ أَقْوَامٍ يَرْفَعُونَ أَبْصَارَهُمْ إِلَى السَّمَاءِ فِي صَلاَتِهِمْ»، فَاشْتَدَّ قَوْلُهُ فِي ذَلِكَ، حَتَّى قَالَ: «لَيَنْتَهُنَّ عَنْ ذَلِكَ أَوْ لَتُخْطَفَنَّ أَبْصَارُهُمْ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 750]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Meke damun wasu mutane ne suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallarsu". Sai maganrasa ta yi tsanani a kan hakan, har ya ce: "Kodai su hanu daga hakan ko a fauce magannansu".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 750]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗi waɗanda suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallah a lokacin addu'a ko waninta, sannan tsawatarwarsa ta yi tsanani da narkonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wanda ya aikata haka da cewa shi yana jin tsoro akan idanuwansu kada a fauce musu su a karɓesu da gaggawa ta inda basa ji sai kawai ga shi sun rasa n'imar gani.