عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أَسْوَأُ النَّاسِ سَرَقَةً الَّذِي يَسْرِقُ صَلَاتَهُ» قَالَ: وَكَيْفَ يَسْرِقُ صَلَاتَهُ؟ قال: «لَا يُتِمُّ رُكُوعَهَا، وَلَا سُجُودَهَا».
[صحيح] - [رواه ابن حبان] - [صحيح ابن حبان: 1888]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta".
[Ingantacce ne] - [Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi] - [صحيح ابن حبان - 1888]
Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa mafi tsananin mutane muni a sata shi ne wanda yake satar sallarsa; hakan ya kasance ne domin karɓar dukiyar wani wataƙila zai iya amfani da ita a duniya, saɓanin wannan satar, domin ya saci haƙƙin kansa na sakamako da lada, suka ce: Ya Manzon Allah, ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: Ba ya cika ruku'unta kuma ba ya cika sujjadarta; hakan yana nufin ya yi gaggwa a ruku'u da sujjada, ba zai zo da su ba a kan cikkakkiyar fuskar su ba.