عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عنه سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَقُولُ:
«قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: {الْحَمْدُ لِلهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ}، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: {الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ}، قَالَ اللهُ تَعَالَى: أَثْنَى عَلَيَّ عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: {مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ}، قَالَ: مَجَّدَنِي عَبْدِي، -وَقَالَ مَرَّةً: فَوَّضَ إِلَيَّ عَبْدِي-، فَإِذَا قَالَ: {إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ}، قَالَ: هَذَا بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ: {اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ، صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلا الضَّالِّينَ}، قَالَ: هَذَا لِعَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 395]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Allah - maɗaukakin sarki Ya ce: Na raba sallah tsakanina da tsakanin bawaNa gida biyu, bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan bawa ya ce: {Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: bawaNa ya godemin, idan ya ce: {Mai kyauta a duniya mai jin ƙan muminai a lahira}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: BawaNa ya yabeni, idan ya ce: {Mamallakin ranar sakayya}, Zai ce: BawaNa ya girmamaNi, - wani lokaci kuma ya ce: bawaNa ya fawwala (al'amuransa) gareNi -, idan ya ce: {Kai kaɗai muke bautawa, kuma gareka kaɗai muke neman taimako}, sai Ya ce: Wannan tsakanina da tsakanin bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan ya ce: {ka shiryar da mu hanya madaidaiciya, hanyar waɗanda Ka yi ni'ima a garesu ba waɗanda Ka yi fushi a kansu ba, ba kuma ɓatattu ba}, zai ce: Wannan ga bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 395]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa a hadisi Qudsi: Na raba Surar fatiha a sallah gida biyu tsakanina da tsakanin bawaNa, rabinta nawa ne, rabinta kuma nasane.
Rabinta na farko: Godiya ne da yabo da girmama Allah, zan saka masa da mafificin sakamako.
Rabinta na biyu: Ƙanƙar da kai ne da addu'a, zan amsa masa, kuma zan ba shi abin da ya roƙa.
Idan mai sallah ya ce: {Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}, Allah zai ce: BawaNa ya gode min, idan ya ce; {Mai kyauta a duniya Mai jin ƙan muminai a lahira}, Allah zai ce: BawaNa ya yabeni, sai ya yabeNi ya yi iƙirari da gamewar baiwa ga halittata, idan ya ce: {Mamallakin ranar sakamako}, Allah zai ce: BawaNa ya girmamaNi, ita ce ɗaukaka mayalwaciya.
Idan ya ce: {Kai kaɗai muke bautawa, kuma gareka ne kaɗai muke neman taimako}, Allah zai ce: Wannan tsakanina ne da tsakanin bawaNa.
Ɓangare na farko daga wannan ayar shi ne: {Kai kaɗai muke bautawa} shi ne iƙirari da Allantakar Allah, da kuma amsawa ga yin bauta, da shi ne ɓangaren da yake ga Allah ya kare.
Ɓangare na biyu daga ayar shi ga bawa ne: {Gareka ne kaɗai muke neman taimako} neman taimako daga Allah ne, da kuma alƙawarinSa na taimako.
Idan ya ce: {Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya* Hanyar waɗanda Ka yi ni'ima garesu, ba waɗanda Ka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba}, Allah zai ce: Wannan ƙanƙar da kai ne da addu'a daga bawaNa, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa, haƙiƙa na amsa addu'arsa.