عَنْ عُبَادَةَ بْنِ الصَّامِتِ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَا صَلَاةَ لِمَنْ لَمْ يَقْرَأْ بِفَاتِحَةِ الكِتَابِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 756]
المزيــد ...
Daga Ubadah dan Samit - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Babu sallah ga wanda bai karanta Fatiha ba".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 756]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa sallah ba ta inganta sai da karanta suratul Fatiha, ita rukuni ce daga rukunan sallah a kowace raka'a.