عن جابرٍ رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول:
«إِنَّ بَيْنَ الرَّجُلِ وَبَيْنَ الشِّرْكِ وَالْكُفْرِ تَرْكَ الصَّلَاةِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 82]
المزيــد ...
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 82]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargaɗi game da barin sallar farilla, ya ba da labarin cewa tsakanin mutum da afkawa a shirka da kafirci (shi ne) barin sallah, sallah ita ce rukuni na biyu daga rukunan musulunci, al'amarinta mai girma ne a musulunci, wanda ya barta yana mai musun wajabcinta, to, ya kafirta da ijima'in musulmai, idan ya barta gabaɗaya don wulaƙantarwa da kasala, to, shi kafiri ne, an cirato ijma'in sahabbai a kan hakan, idan ya kasance yana bari wani lokaci wani lokaci kuma yana yin sallah, to, ya kai kansa ga wannan narkon mai tsanani.