عن بريدة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«إِنَّ الْعَهْدَ الَّذِي بَيْنَنَا وَبَيْنَهُمُ الصَّلَاةُ، فَمَنْ تَرَكَهَا فَقَدْ كَفَرَ».
[صحيح] - [رواه الترمذي والنسائي وابن ماجه وأحمد] - [سنن النسائي: 463]
المزيــد ...
Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -:
"Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta".
[Ingantacce ne] - - [سنن النسائي - 463]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa alƙawari tsakanin musulmai da wasunsu daga kafirai da munafikai (shi ne) sallah, wanda ya barta to haƙiƙa ya kafirta.