+ -

عن عمران بن حصين رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«‌لَيْسَ ‌مِنَّا ‌مَنْ ‌تَطَيَّرَ أَوْ تُطُيِّرَ لَهُ، أَوْ تَكَهَّنَ أَوْ تُكُهِّنَ لَهُ، أَوْ سَحَرَ أَوْ سُحِرَ لَهُ، وَمَنْ عَقَدَ عُقْدَةً، وَمَنْ أَتَى كَاهِنًا فَصَدَّقَهُ بِمَا يَقُولُ فَقَدْ كَفَرَ بِمَا أُنْزِلَ عَلَى مُحَمَّدٍ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ».

[حسن] - [رواه البزار] - [مسند البزار: 3578]
المزيــد ...

Daga Imaran Ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
Ba ya cikimmu wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ko ya yi bokanci ko aka yi masa bokanci, ko ya yi tsafi ko aka yi masa tsafi. Duk wanda ya ƙulla wani ƙulli, duk wanda ya je wurin boka ya gasgata shi a kan abin da ya faɗa, to, ya kafircewa abin da aka saukar ga (Annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

[Hasan ne] - [Bazzar ne Ya Rawaito shi] - [مسند البزار - 3578]

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi alƙawarin narkon azaba ga wanda ya aikata wasu ayyuka cikin al’ummarsa, da ya ce: Ba ya daga cikimmu.
Na farko: Wanda ya yi camfi ko aka yi masa camfi, asalinsa: suna sakin tsuntsu ne lokacin fara wani abu, kamar tafiya ko fatauci ko wanin haka, idan ya yi dama sai ya ce akwai sa’a, sai ya yi abin da ya sa a gaba, idan kuma ya yi hagu sai ya ce babu sa’a sai ya ƙi yi, bai halatta ya yi haka da kansa ba, ko ya sa a yi masa, camfi da kowanne abu na ji ne ko na gani ya shiga ƙarƙashin haka, da tsuntsaye ko dabbobi aka yi, ko masu fama da nakasa, ko wasu lambobi ko ranaku, da sauransu.
Na biyu: Wanda ya yi bokanci ko aka yi masa bokanci’. Duk wanda ya ce ya san gaibu ta hanyar taurari, ko wanin haka, ko ya je wurin wanda ya ce ya san gaibu kamar boka da makamantansu, ya kuma gasgata shi a abin da ya faɗa na cewar ya san gaibu, to, haƙiƙa ya kafirta da abin da aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Na uku: Wanda ya yi asiri ko aka yi masa asiri’. Shi ne wanda yake yin a siri da kansa, ko ya sa a yi masa asiri, domin ya amfanar da wani da shi, ko don ya cutar da wani, ko ya ƙulla ƙulli da zare da asiri da surkulle da aka haramta da tofi a kai.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wajibcin dogaro ga Allah, da imani da abin da Allah Ya hukunta Ya kuma ƙaddara. Da kuma haramcin camfi da asiri da bokanci, ko tambayar masu yin haka.
  2. Iƙirarin sanin gaibu ɓangare ne na shirka, wanda yake kore Tauhidi.
  3. Haramcin gasgata bokaye da zuwa wurinsu, kuma yana shiga nan duba a tafin hannu, da kwarya da buruji da nazari a kansu, ko da kuwa don leƙawa ne.